IQNA

Hamas Ta Yi Kiran Zanga-Zanga A Gobe Juma'a

23:35 - July 20, 2017
Lambar Labari: 3481719
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Hamas ta yi kira zuwa ga gagarumar zanga-anga a gobe Juma'a a dukkanin fadin Palastinu.

Kamfanin dillancin iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alalam cewa, a yau kungiyar gwagwarmayar Palastinawa ta Hamas ta yi kira zuwa ga gagarumar zanga-anga a gobe Juma'a a dukkanin zirin Gaza da kuma yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Bayanin ya ce manufar wannan jerin gwano a gobe Jum'a shi ne bayyana wa duniya halin masallacin Quds mai alfarma yake ciki a hannun yahudawa, tare da hana musulmi gudanar da sallar Juma'a.

Haramtacciyar kasar Isra'ila tare da cikakken goyon bayan Amurka da wasu daga cikin larabawa 'yan shata ga Amurka, tana ci gaba da cin karenta babu babbaka akan al'ummar Palastine, tare da keta alfarmar wurare masu tsarki da ke wurin.

3621129


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha