IQNA

Hasumiyar Masallci Mafi Jimawa A Arewacin Afirka Ta Rushe

23:41 - July 23, 2017
Lambar Labari: 3481727
Bangaren kasa da kasa, hasumiyar masallaci mafi jimawa ayankin arewacin Afirka da ke garin Aujlaha kilomita 400 a kudancin Benghazi Libya ta rushe.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ansamed ya bayar da rahoton cewa, masu gudanar da ayyukan raya wuraren tarihi na kasar Libya sun isa wannan wuri domin ganin yadda za a gudanar gyara.

Wannan masallaci dais hi ne mafi jimawa ayankin arewacin Afirka, wanda aka gina shit un lokacin sarakunan daular fatimiyyah, wanda aka gina a cikin shekara ta 474 na hijira kamariyyah, a lokacin khalifan Fatimiyyah Mustansir billah, wanda ya mutu a birnin Alkahira na kasar Masar.

Fadin wannan hasumiya ya kai mita 5 da santimita 10, kamar yadda kuma take da tsawon da za a iya hango ta daga nesa, kuma jama’a da dama suna kallon wannan masallaci a matsayin abin tarihi da alfahari a gare su, amma saboda jimawa da kuma yanayin isa da ruwan sama, wannan yasa abana hasumiyar ta fadi.

Tsawon hasumiya baki daya ya kai mita 25, kuma mutane suna zuwa wannan wuri daga gabshin Afirka zuwa yammacinta, da kuma dukkanin yankuna na arewacin nahiyar.

3621920


captcha