IQNA

Yada Madaidaicin Ra’ayi Shi Ne Manufar Radiyon Kur’ani Na Aljeriya

23:43 - July 23, 2017
Lambar Labari: 3481728
Bangaren kasa da kasa, gidan radiyon kur’ani na kasar Aljeriya na gudanar da bikin cikarsa shekaru 26 da kafawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mishwar siyasi cewa, babbar manufar manufar kafa wannan radiyo it ace yada koyarwa ta kur’ania tasakanin msuulmi na wannan kasa.

A wannan lokaci da ake gudanar da tarukan cikar shekaru 26 da kafa wannan gidan radiyo, mahukuntan wurin sun bayyana cewa, a halin yanzu gidan radiyon yana yin kokari matuka domin wayar da kan musulmi dangane da muhimmancin yin addini ta hanyar da ta dace kamar yadda kr’ani ya koyar.

Bayanin ya ce matasa da ake saurin sauya musu tunani da sunan addini, su ne wadanda shirye-shiryen suka mayar da hankali a kansu, domin ganin an samu daidaitoa cikin tunaninsu, maimakon yin wasa da hankulansu da juya kwakwalensu yadda aka dama ana saka su cikin ayyukan ta’addanci da sunan addini.

Hamdi Isa shi ne babban darakta na wannan tashar radiyo ya bayyana cewa, dole ne su yi amfani da wannan damar domin isar da sakon musulunci na zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi su nkansu da suke da banbancin fahimta a kan abubuwa daban-dabam, da kuma samar da fahima da zaman lafiya tsakanin musulmi da wadanda ba musumi ba.

3621669


captcha