IQNA

Taron Wadanda Ba Musulmi Ba A Cibiyar Muslunci A Amurka

23:20 - July 24, 2017
Lambar Labari: 3481732
Bangaren kasa da kasa, cibiyar musulmia a jahar Illinois a kasar Amurka ta gayyaci wadanda mamuslmi domin halartar taronda ta shirya.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na daily-chronicle cewa, wannan cibiyar ta shirya wannan taron ne a jiya tare da halartar wasu cikin mazauna yankin.

Wanann gayyata dai an yi ta ne ga kowa duk mai bukatar halartar wurin, domin ganewa idanunsa wasu daga cikin irin ayykan da musulmi suke gudanarwa a wurin, da kuma amsa tambayoyi dangane da addinin muslunci.

Baya ga haka kuma cibiyar tya bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka halarci wurin, da nufin kara samar da yanayi na zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin msuulmi da wadanda ba msuulmi ba.

Wannan mataki ya zo ne sakamakon irin matsalolin da ake samu a Amurka a wannan lokaci na nuna tsananin kyama ga musulmi, sakamakon irin matakan da gwamnatin kasar take dauka na nuna kyama ga musulmi a hukumance.

3622442

Taron Wadanda Ba Musulmi Ba A Cibiyar Muslunci A Amurka

Taron Wadanda Ba Musulmi Ba A Cibiyar Muslunci A Amurka

captcha