Jaridar Independent ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, wannan kirista mai suna Nedal Abbud ya shiga cikin sahun salla ne yana karanta littan adduu'oi na addinin kirista, domin nuna cikakken goyon bayansa ga musulmi Palastinawa a kan zaluncin da suke fuskanta daga yahudawan Isra'ila.
Nedal Abbud ya ce musulmi 'yan uwansa ne, a kan haka dole ne ya nuna goyon bayansa a gare su ko ta wace hanya, kuma cewarsa zai ci gaba da bayar da goyon bayansa a gare su da kuma yin Allah wadai da keta alfarmar masallacin Quds da yahudawan Isra'ila ke yi.
3622900