IQNA

Al Saud Na Ci Gaba Da Kaddamar Da Farmaki Kan Al'ummar Awamiyyah

17:30 - July 27, 2017
Lambar Labari: 3481742
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron masarautar Al Saud suna ci gaba da kaddamar da farmaki a kan al'ummar birnin Awamiyyah da ke cikin gundumar Qatif a gabashin Saudiyyah.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Shafin yada labarai na Al'ahd News ya bayar da rahoton cewa, a jiya jami'an tsaron masarautar Al Saud sun kai farmaki a kan wasu unguwanni a cikin birnin Awamiyya na mabiya mazhabar shi'a, inda suka yi ta yin harbe-harbe na kan mai uwa da wabi da kuma harba makaman roka a kan gidajen jama'a fararen hula.

Rahoton ya ce mutane da dama sun jikkata, yayin da waus suke cikin mawuyacin hali, sakamakon shakar isakar gas da jami'an tsaron suke fesawa wanda ke dauke lumfashi, musamman ma ga masu matsaloli na musamman da suka shafi lumfashi.

Yanzu haka mahukuntan masarautar Al Saud da ke rike da madafun iko a kasar suna shirin fille kawunan wasu fararen hula sha hudu daga wannan yanki, bisa zarginsu da shiga jerin gwanon nuna rashin gamsuwa da salon mulkin Al Saud.

Al'ummar yankin gabashin Saudiyya dai mabiya mazhabar shi'a ne, kuma suna yin korafi ne dangane da yadda aka mayar da su saniyar ware, tare da haramta musu hakkokinsu na 'yan kasa, duk kuwa da cewa dukkanin arzikin man fetur da iskar da tattalin arzikin kasar ya dogara da shi, ana fitar da su ne daga yankinsu.

3623419


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha