IQNA

Taron Idin Ghadir A Masallacin Los Angeles

23:38 - September 10, 2017
Lambar Labari: 3481882
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron idin Ghadir a masallacin Los Angeles a masallacin Al-zahra tare da jefa furanni dubu daya da 110.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a jiya an gudanar da gagarumin taron idin Ghadir a masalalcin Zahra da ke yankin Los Angeles na kasar Amurka, tare da halartar daruruwan musulmi har ma da wadanda ba musulmi ba.

Hojjatol Islam Ruhollah Jidi shi ne ya gabatar da jawabia wurin taron, wanda kuma shi ne limamain masallacin Zahra, inda ya bayyana Ghadir a matsayin ranar da Allah madaukakin sarki ya cika addininsa ga bayinsa.

Ya ci gaba da cewa, dukkanin abin da ya faru a ranar Ghadir ba ya faru ba ne ba tare da huikima ba, domin kuwa dukkanin lamarin Allah yana tare da hikima, kuma baya umarta manzonsda da wani abu face abin da yake daidai kuma bisa hikima.

A Ranar Ghadie manzon Allah ya tsayar da dukkanin musulmi a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan kammala a ikin hajji, inda ya bayyana cewa duk wanda ya kasance waliyi a gare shi, to yanzu Aliyu ne majibincin lamarinsa, yana mai tabbatar da shia matsayin khalifansa a bayansa.

Dukkanin sahabban manzon Allah da suke a wurin sun yi ta taya Aliyu murna tare da yin mubaya’a a gare shia matsayin khalifan manzon Allah a duk lokacin da Allah ya karbi manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

3640208


captcha