IQNA

A Karon Farko Musulma Ta Zama Shugabar Singapore

17:19 - September 13, 2017
Lambar Labari: 3481891
Bangaren kasa da kasa, Halima Yakubu musulma 'yar asalin Malaye ta zama shugabar kasa a Singapore.
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa, ita kadai ce 'yar takara da ka mika sunanta ga kwamitin zaben shugaban kasa, wadda kuma aka amincewa da ita.

Halima Yakub dai ta kasance a majalisar dokokin kasar tun fiye da shekaru ashirin da suka gabata, daga bisani kuma ta zama ita ce shugabar majalisar.

Wannan dai shi ne karon farko da mace musulma ta zama shugabar kasa a wannan kasa da ke gabashin nahiyar asia.

Kasar Singapore mai adadin mutan ekimanin miliyan 5.5, ta samu 'yancin kanta ne shekarar 1965 daga kasar Malaysia.

3641483


captcha