Kamfanin dillanacin labaran iqna ya habarta cewa, Umar Faruk jakadan musulmin Myanmar a kasar Masar ya bayyana cewa, a lokutan baya har zuwa shekara ta 1800 musulmi ne suke iko da yankin Rakhin, inda su ne suke da hakkin nada sarakunan yankin, amma daga lokacin zuwa gwamnatin Burma a cikin shekara ta 1973, daa lokacin aka fara cutar da musulmi tare da mayar da su saniyar ware.
Ya ce duk da cewa adadin musulmin Rohingya ya haura miliyan biyu da rabi a halin yanzu, amma adadin wadanda aka kasha daga fara kaddamar da ahri a kansu a cikin shekara ta 2016 ya zuwa yanzu, ya haura dubu biyar.
Umar Faruk y ace Aung Suu Kyi ita ce a matsayin Hitler ta wannan zamani.