IQNA

Mutane 4 Suka Rasa Rayukansu A Wani hari A Kasar Kamaru

20:42 - September 14, 2017
Lambar Labari: 3481893
Bangaren kasa da kasa, akalla mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kasar Kamaru.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin hosted cewa, ya amabto majiyar tsaron kasar ta Kamaru tana cewa; Wata buduruwa ce ta kai harin a kusa da masallacin Sandawadjiri da kusa da iyakar Najeriya.

Majiyar ta kara da cewa; Baya ga fararen hula 4 da suka kwanta dama, ita kanta wacce ta kai harin ta halaka.

Hare-hare irin wadannan dai ana danganta su ne da kungiyar boko haram.

Arewacin kasar Kamaru wanda yake da iyaka da Najeriya da kuma kasar chadi yana da yankunan da kungiyar ta boko haram take tsananta kai hare-hare.

A bisa rahoton Majalisar Dinkin Duniya Kamaru ce kasa ta biyu bayan Najeriya da kungiyar ta boko hari take tsananta kai wa hari.

3641872


captcha