IQNA

Amurka Taki Yin Allah Wadai Da Kisan Musulmin Myanmar

21:02 - September 14, 2017
Lambar Labari: 3481896
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Amurka taki yin Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi wa msuulmin kasar Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklto daga shafin yada labarai na kamfanin dillancin labaran Anatoli AA cewa, tun bayan da aka fara yi wa musulmin kasar Myanmar kisan gilla a hannu dakarun gwamnatin kasar da ‘yan addinin buda, har inda yau take Amurka bata yi Allah wadai da hakan ba.

Mai magana da yawun ma’aktar harkokin wajen kasar Amrka ta bayyana abin da yke faruwa a Myanmar da cewa yana sosa rai, inda ta tsaya anan kawai.

A lokacin da aka tambaye ta ko hakan yana a matsayin kisan kiyashia kan musulmi ‘yan kabilar Rohingya, sai ta bayyana cewa Amurka ba za ta kira abin da yake faruwa a Myanmar da haka ba.

A kwanakin baya ma babban jami’in gwamnatin murka mai kula da harkokin yankin Asia ta gabas ya bayyana cewa, basu ganin laifin gwamnatin Myanmar kana bin da yake faruwa na kisan musulmin kasar, kuma ba za su amince da matsin lamar duniya akan gwamnatin Myanmar ba.

3641948


captcha