IQNA

Ganawar Babban Sakataren Hizbullah Da Ayatollah Nuri Hamedani

21:16 - September 15, 2017
Lambar Labari: 3481897
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah ya gana da Ayatollah Nuri Hamedani a ziyarar da ya kai Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin alalam cewa, a yau Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah ya gana da Ayatollah Nuri Hamedani a yau a ofishin malamin da ke birnin Neirut.

A yayin ganawar, sayyid Nasrillah ya bayyana wannan ziyara ta babban malami a matsayin ziyara da take cike da albarka, haka nan kuma y aba shi bayani dangane da halin da ake ciki dangane da shiri gwagwarmaya.

Sayyid Nasrullah ya jinjinawa wannan babban malamin addini, musamman a kan irin goyon bayan da yake baiwa gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon wajen kare kasarsu daga mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ‘yan ta’adda.

Haka nan kuma ya yi ishara da yakin tsawon kwanaki 33 daka yi tsakanin haramtacciyar kasar yahudu da kuma Lebanon, inda wannan babban malami ya kasance a sahun gaba wajen mara baya ga kungiyar Hizbullah tare da yin kira na bayar da duk wani taimako ga kungiyar.

A nasa bangare Ayatollah Nuri Hamedani ya bayyana Sayyid Hassan Nasrulllah a matsayin malami mai gwagwarmaya mai gaskiya a cikin a cikin dukkanin lamurransa, kamar yadda kuma yake a matsayin abin koyi ga dukkanin masu gwagwartmaya na duniya.

Haka nan kuma malamin ya kara jaddada cewa za su ci gaba da goyon bayan Hizbullah da ma sauran masu gwagwarmayar yaki da zalnci da tabbatar da adalci, domin wanan shi ne abin da Amirul muminin (AS) magajin manzon Allahya koyar.

3642139


captcha