IQNA

Larijani A Ganawa Da Takwaransa Na Belgium:

Matsalar Ta’addanci Na Barazana Ga Iran Da Belgium / Dole A kawo Karshen Matsalolin Myanmar Da Yemen

22:09 - September 16, 2017
Lambar Labari: 3481903
Bangaren siyasa, Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Yaki da ta'adda da nufin kawo karshensa yana bukatar samun hadin kan kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A taron manema labarai da ya gudanar da takwararsa na kasar Belgium a yau Asabar a birnin Tehran: Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci na Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa a zaman tattaunawansu sun fi maida hankali ne kan hadin kai da taimakekkeniya tsakanin kasashen Iran da Belgium musamman a fagen wanzar da zaman lafiya da sulhu a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda suka tattauna batun matsalar kasashen Yamen da Myanmar tare da jaddada muhimmancin samun hadin gwiwa a fagen yaki da ta'addanci a tsakanin kasshensu.

A nashi bangaren shugaban Majalisar Dokokin Kasar Belgium Siegfracke ya bayyana cewa: Kungiyar Tarayyar Turai bata amince da dukkanin siyasar kasar Amurka ba, don haka kasar Bengium tana jaddada bukatar hanzarta bude ofishin kungiyar Tarayyar Turai a kasar Iran.

Kasashen turai da dama suna fuskantar barazana ta ayyukan ta’addanci daga ‘yan ta’adda da suke dawowa daga kasashen duniya, nda suke yin barazana ga zaman lafiyar wadannan kasashe.

Tun kafin wannan lokacin dai an gargadi kasashen turai masu mara baya ga ‘yan ta’adda domin cimma burin a siyasa, da cewa su kwana da sanin cewa wadanna yan ta’adda za su dawo a kansu.

3642471


captcha