IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali:

Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga Duk Wani Karen Tsaye Ga Yarjejeniyar Nukiliya

23:18 - September 17, 2017
Lambar Labari: 3481904
Bangaren kasa da kasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunne da cewa Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya da ta cimma da manyan kasashe to sai dai za ta mayar da martani ga duk wani karen tsaye ga yarjejeniyar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi wajen bikin yaye daliban makarantar 'yan sanda ta Iran, inda yayin da yake magana kan yarjejeniyar nukiliyan ya ce al'ummar Iran suna nan tsaye kyam kan kafafunsu kan yarjejeniyar nukiliyan, to amma duk wani kokarin karya yarjejeniyar daga wajen ma'abota girman kan duniya zai fuskanci mayar da martanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka nan yayin da yake magana kan maganganun da matakan da gwamnatin Amurka take dauka dangane da yarjejeniyar nukiliyan, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Amurkawa suna nuna wannan mugunta da kiyayya ta bangarori daban-daban dangane da wannan batu na yarjejeniyar nukiliya, wanda hakan yana dada tabbatar da abin da Imam Khumaini (r.a) ya fadi dangane da Amurkan ne na cewa ita Babbar Shaidaniya ce.

Ayatullah Khamenei ya ce Iran ta fara shirin nukiliyanta na zaman lafiya ne bayan da masanan kasar suka ce tana bukatar alal akalla megawatt 20,000 na makamashin nukiliya din, to amma Amurka tana adawa da hakan saboda tsohuwar gabar da take da shi kan duk wani abin ci gaba na al'ummar Iran da sauran al'ummomin duniya.

Yayin da ya koma kan batun matsalar tsaro da ake fuskantar a yankin nan kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya dora alhakin hakan kan Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila saboda bakar aniyar da suke da ita na mamaya.

Gwamnatin kasar Amurka dai tana barazanar na ficewa daga yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran, bisa hujjar cewa Iran tana gudanar da ayyukan makamai masu inzami, wanda acewar murka wannan ya saba wa yarjejeniya da aka cimma kan shirin Iran na nukiliya.

A nata bangaren Iran bayyana irin wanan furuci da cewa yana kara tabbatar da jahilcin jami’an Amurka na wannan gwamnati mai ci yanzu kan yarjejeniyar nukiliya, inda Iran takan bukace da su je su sake karanta abin da yarjejeniyar ta kunsa kafin su yi duk wani furuci a kan jahilci.

3642993


captcha