IQNA

Wilder Ya Bukaci:

A Share Addinin Musluci Daga Cikin Addinai Masu 'Yanci A Holland

23:24 - September 17, 2017
Lambar Labari: 3481906
Bangaren kasa da kasa, Geert Widers shugaban jami'aiyyar masu ra'ayin 'yan mazana jiya Holland ya bukaci da acire addinin muslunci daga cikin addinai masu 'yanci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafin kamfanin dillancin labaran Anatoli cewa, Geert Widers shugaban jami'aiyyar masu ra'ayin 'yan mazana jiya Holland ya bukaci da acire addinin muslunci daga cikin addinai masu 'yanci na gudanar da harkokinsu.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zanatawa da jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya, inda ya bayyana cewa hakika yana da burin ganin an dauki matakan da suka dace wajen dakile addinin musluncia kasar ta Holland.

Ya ce muslucni ba addini ba ne, wata akidace kawai ta tsatsauran ra'ayi, wanda idan ba ataka mata birrki ba za ta ci gaba da yaduwa a cikin kasashen turai, wanda hakan yana tattare da bababn hadari a cewarsa.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, a duk lokacin da ya samu nasarar lashe shugabancin kasar ta Holland zai haramta addinin muslunci a kasar baki daya, tare da rufe dukkanin masallatai da makarantun muslunci da ke cikin kasar.

Yanzu haka dai wannan mutum ya samu kujeru 20 daga cikin kujeru 150 na majalisar dokokin kasar.

3642693


captcha