Wannan rahoto y ace fiye da mutane dubu 400 ya zuwa suka tsallaka cikin kasar Bangaladesh, yayin da wasu dubban kuma suka mutu ta hanyar kisan da sojoji da kuma 'yan addinin buda suke yia kansu, wasu kuma sun mutu a hanya, wasu kuma sun nutse a cikin ruwa.
Halin da musulmin Myanmar suke ciki yan ata kara munana sakamakon rashin samun wadataccen abinci da kuma kayan bukatar rayuwa a cikin sansanonin da aka tsugunnar da su.