IQNA

Dubban Yahudawa Sun kai Farmaki A Masallacin Annabi Ibrahim

17:34 - September 18, 2017
Lambar Labari: 3481910
Bangaren kasa da kasa, yahudawa kimanin dubu uku ne suka kutsa kai a cikin masallacin annabi Ibrahim da ke garin Alhalil a Palastinu tare da keta alfarmar wannan masallaci mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na PNN ya bayar da rahoton cewa, a jiya dubban yahudawa ne suka kutsa kai a cikin masallacin annabi Ibrahim da ke garin Alhalil a Palastinu tare da keta alfarmar wannan masallaci mai alfarma bisa hujjar cewa lokacin idin yahudaw ayana karatowa.

Wannan bas hi ne karon farko da yahudawa suke yin haka ba, domin kuwa shekarun baya-bayan sukan isa wanann masallaci mai alfarma domin tsokanar musulmi da sunan raya ranakun idin yahudawa.

Masallacin annabi Ibrahim yana daga cikin muhimman wurare na musulmi masu tsohon tarihi da ke cikin Palastinu, wadanda yahudawa ke ta hankoron ganin sun mayar da su a matsayin wurare mallakinsu.

Yanzu haka yahudawa suna ci gaba da killace wannan masallaci tae da keta alfarmarsa inda suke raye-raye da sauran ayyukan yahudawa a cikinsa, kuma a lokaci guda suna samun kariya daga jami'an tsaron yahudawa.

A shekarun baya ma wani bayahude ya kai farmaki kan musulmi a okacin sallar asubahi, inda ya kasha masallata fiye da ashirina cikin masallacin.

3643430

 

 

 

captcha