IQNA

Baje Kolin Hotunan Arbaeen

Baje kolin hotuna na tsawon kwanaki 10 a jere a dandalin Imam Hussain (AS) da ke birnin Tehran, tare da taimakon wasu kungiyoyin Irakawa na Samawah. Wannan baje koli zai kunshi allunan hotuna 300 tun daga shekaru 4 da suka gabata da aka fara yin tattaki da kuma yin hidima ga masu ziyarar Sayyidu shuhada (AS) wadanda Mujtaba Haidari ya dauka. Wadanna hotuna an fara daukarsu ne tun a shekara ta 2013 har zuwa 2016, da ke nuna yadda ake gudanar da wannan tattaki.