IQNA

Jagoran Juyi A Taron Dalibai Masu Makoki:

Hankoron Matasa Na Riko Da Koyarwar Juyi Wata Bushara Ce Ta Alkhairi

23:03 - November 09, 2017
Lambar Labari: 3482081
Bangaren siyasa, a yayin gudanar da taron juyayin arbaeen na Imam Hussain (AS) a Husainiyar Imam Khomeni (RA) jagoran juyin juhalin musuluci ya kasance a cikin mahalarta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin gudanar da taron juyayin arbaeen na Imam Hussain (AS) jagoran juyin juhalin musuluci tare da wasu daga cikin manyan malamai dajami’an sun samu halartar wurin.

Ayatollah Sayyid ali hamenei ya yi nuni da cewa, Imam Hussain (AS) ya kasance maikoyar da addini a aikace ta hanyar magana da kuma aiki da sadaukantarwa, koyi da shi bai takaitu da taruka ba, yin koyi da shi a cikin aiki da aikata umarninsa da hanuwa daga hanninsa shi ne aiki da marnin addini da hanuwa daga hanin addini, domin kuwa shi yana wakiltar manzon Allah ne.

A nasa bangaren Hjjatol slam Pnahiyan ya gabatar da jawabi, wanda shi ma ya ja hankulan duban matasa samari daliban jamioi daban-daban da suka taru a wurin, inda ya bayyana muhimmancin yin koyi da Imam Hussain (AS) a matsayin koyi da abin da manzon Alah ya koyar.

Haka nan kuma ya jadda ewa, imani da tsoron Allah da kuma yin aiki domin neman yardarm Allah a kowane lokaci suna kan gaba a cikin darussan da rayuwar Imam Hussain (AS) ke koyarwa.

A yau ne miliyoyin musulmi suke gudanar da tarukan arbaeen na Imam Hussain (AS) a hubbarensa da ma sassa na duniya, domin tunawa da wakia’r da ta auku a kan iyalan gidan manzo.

3661648


captcha