IQNA

Taron Makokin Wafatin Manzon Allah A Kasar Holland

16:56 - November 16, 2017
Lambar Labari: 3482107
Bangaren kasa da kasa, cibiyar raya al’adun musulunci Akausar za ta shirya taron tunawa da wafatin manzon Allah (SAW).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar raya al’adun musulunci Akausar za ta shirya taron tunawa da wafatin manzon Allah (SAW) a brnin Hague, da kuma zagayowar shahadar Imam Hassan Mujtaba (AS) a babban ginin cibiyar.

Wannan cibiya ta mabiya mazhabar shi’a Ahlul bait a kasar Halland, ta kan dauki nauyin shirya tarukan addini musamman wadanda suka shafi gayowar haihuwa ko wafatin manzon Alah da ahlul bait.

Taron zai gudana ne a ranar Asabar mai zwa, inda za a gabatar da jawabai a wasu bangarori kan matsayin manzon Allah (SAW) da kuma Imam Hassan (AS) Sayyid Ali Sa’abari ne zai gabatar da jawabi.

An kebance wuri na musamamn wanda maza za s zauna, kamar yadda kuma aka kebance wani wurin na mata zalla.

Haj Muhammad Samawi wani mai yabo ga manzon Alah da kuma Ahlul bait, zai halarci wurin, kuma zai gabatar da kasidu na musamman da suka kebanci wannan munasaba.

3663583


captcha