IQNA

Ayatollah Imami Kashani A Yayin Hudubar Juma’a:

BMurabus Din Hariri Na Nuni Da Sabon Shirin Makiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya

23:34 - November 17, 2017
Lambar Labari: 3482108
Bangaren kasa da kasa, wanda ya jagoranci sallar Juma’a ayau a birnin Teran ya bayyana cewa makiya musulmi da ma al’ummomin yanin gabas ta tsakiya suna da wan shirin da suke son aiwatarwa a lokacin nan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Limamin na Tehran ya yi ishara da makircin makiyan al'ummar musulmi sannan ya kara da cewa; Wajibi ne ga al'ummar musulmin da su hade kawukansu domin fuskantar makiyan.

Ayatullah Muhammad Imami Kashani ya yi ishara da murabus din pira ministan kasar Lebanon Sa'ad al-Haririna kasar Lebanon, tare da cewamanufar makiya ita ce hargitsa zaman lafiyar kasar.

Limamin ya yi ishara da hikimar babban magatakardar Kungiyar Hizbullah akan batun murabus din, tare da cewa hakan yakashe wutar rikicin da Saudiyya da 'yan Sahayoniya suka kitsa.

Limamin na Tehran ya ce makiya ba su tsammaci al'ummar ta Lebanon za su hada kansu wuri daya ba akan batun murabus din Sa'adul hariri.

Makwanni biyu da suka gabata ne dai pira ministan na Lebanon ya yi murabus daga kasar Saudiyya abinda gwamnati da al'ummar kasar suka dauka a matsayin tsoma bakin kasar Saudiyya a harkokin cikin gidansu.

Kafofin yada labarai da dama na haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da bullar sabon kawacen da ya fito a fili tsakanin Isra’ila da Saudiyya domin yaki da Iran da kuma kungiyar hizbullah, duk kuwa da cewa dama can akai wannan kawancen boye.

3664267


captcha