IQNA

Juyayin Shahadar Imam Ridha (AS) A Sweden

20:43 - November 19, 2017
Lambar Labari: 3482114
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron juyayin zagayowar okacin shahadr Imam Ridha (AS) a birnin Stockholm na kasar Sweden a daren jiya.
Juyayin Shahadar Imam Ridha (AS) A SwedenKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar musulunci ta Imam Ali (AS) ta shirya gudanar da tarukan juyayin shahadar Imam Rdha (AS) a jiya tare da halartar daruruwan musulmi mabiya tafarkin ahlul bait (as).

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan taro yana daga cikin tarukan addinin muslunci da wannan cibiya take siryawa, domin raya lamarin iyalan gidan manzon Allah (SaW).

An gabatar da jawabai dangane da matsayin Imam Ridha (AS) da kuma darussan da suke a cikin rayuwarsa mai albarka ga dukkanin al’ummar musulmi.

3664781


captcha