Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yaum sabi cewa, Marwa Mahmud Abdulhadi Ubaid wata karamar yarinya ce da ta hardace kur’ani mai tsarki da take da gurin zama malamar kur’ani, Masar wadda sakacin likita ya jawo ta rasa ranta a lardin Dahriyyah na kasar Masar.
Marwawa mai shekaru 11 a duniya, ta kasane mahardaciuar kur’ani wadda ake buga misai da ita a makarantar da ta ke yin karatu.
Mahmud Abdulhadi Ubaid shi ne mahaifinta, ya bayyana cewa an kaita asibiti ne domin yi mata wani dan karamin aiki, inda likitan ya yi amfani da allura mai sanya bac fiye da kima a lokacin aikin, wanda hakan yasa bata tashi ba.
Bayan jira na wani lokaci, mahaifin yarinyar ya bukaci jin halin da diyarsa tae ciki, amma sai aka sanar da shi cewa ta rasu, bayan da ya shiga da kansa a cikin dakin tiayata, ya samu cewa liktan ya gudu.
Yanzu haka dai mahaifin yainyar ya shigar da kara kotu domin bin kadun lamarin, inda yake bayyana hakan a matsayin kisan ganganci.
Bayanai sun nuna cewa wannan likitan ya saba kashe marassa lafiya wajen yin ganganci a cikin aikinsa.