IQNA

Taimakon Cibiyar Muslunci A Stockholm Ga Wadanda Girgiza Kasa Ta Shafa

20:48 - November 19, 2017
Lambar Labari: 3482116
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Stockholm na kasar Sweden ta shiry wani taimako domin al’ummar da girgizar kasa ta shafa a yankin Kermanshah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a antawarsa da Akil Zahiri daya daga cikin shugabannin cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Stockholm na kasar Sweden, ya bayyana cewa wannan cibiya ta shirya wani taimako domin al’ummar da girgizar kasa ta shafa a yankin Kermanshah da ke yamacin Iran.

Wannan taimako dai ya hada da kayan abinci da tufafi da kuma magunguna gami da wasu daga ikin kayyakin bukatar rayuwa, gami da kudade.

Yanzu haka dai mahukuntan kasar Iran sun kafa tantuna inda aka tsugunnar da mutanen da abin ya shafa, kafa a kammala sake gina musu gidajensu, yayin da kuma wadanda suka samu rauknuka ake ci gaba da kula da su a asibitoci.

3664806


captcha