IQNA

Jagora: Jami'ai Su Kara Maida Hankali Ga Wadanda Girgizar Kasa Ta Shafa

22:10 - November 20, 2017
Lambar Labari: 3482117
Bagaren kasa da kasa, a yayin da ya isa yankunan da girgiza kasa ta shafa a cikin lardin Kerman a yau, jagoran juyin juya halin musuunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada kira ga jami’an gwamnati da su kara maida himma wajen ci gaba da tamaka ma wadanda lamarn ya shafa.

Jagoran wanda ya isa a yankin da safiyar yau Litinin, ya soma da ziyartar wuraren da irgizar kasar ta yi barna a birnin Sarpol-e-Zahab, kafin daga bisani ya ziyarci iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu a girgizar kasar data aukawa yankin a cikin daren ranar Lahadin makon da ya gabata

Jagoran ya kuma tattauna da iyalan akan matsaloli da kuma damuwarsu.

Yagoran ya ce yana taya su bakin ciki, kuma shi ma yana ji a jikinsa abunda suke ji a cikin irin wannan yanayi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya kuma yiaddu'a ta samun sauki ga wadanda suka ji raunuka, ya ce lalle ya so ganawa da su amma ba a cikin irin wannan yanayi ba.

A hannu daya kuma jagoran ya bayyana cewa inatare da ku a lokacin da tsohuwar gwamnatin Iraki ta mamaye wannan yankin, inda kuka nuna juriya, to ina son ku nuna mani haka sakamakon wannan iftila'in.

Girgizar kasar mai karfin maki saba’in da digo uku da ta aukawa yankin na Kermanshah a ranar sha daya ga watan nan ta dai yi sanadin mutuwar mutane kimanindari uhudu da shida da raunana wasu dubbai.

3664925

captcha