IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Kai Farmaki Kan Makabarar Annabi Yunus (AS)

22:17 - November 20, 2017
Lambar Labari: 3482118
Bangaren kasa da kasa, daruruwan yahudawan sahyuniya ne suka kai farmaki kan makabartar annabi Yunus (AS) a kusa da garin Alkhalil kudancin kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Press TV ta bayar da rahoton cewa, a ci gaba da cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki, a jiya kimanin yahudawan sahyuniya 300 ne suka kai farmaki kan makabartar annabi Yunus (AS) da ke tazarar kilo mita 5 a wajen garin Alkhalil, tare da keta alfarmar wannan wuri inda kabarin annabi Yunus (AS) yake.

Bayanin ya ci gaba da cewa, yahudawan sahyuniya sun yi wannan aiki na tsokana ne tare da samun cikakken goyon baya da kariya daga jami'an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da yahudawan sahyuniya suka kai farmaki a wannan wuri mai alfarma ba, ko a cikin shekara ta 2015 sun wani abu makamancin hakan, inda wasu daruruwan matasan palastinawa suka nuna rashin amincewarsu, amm jami'an tsaron yahudawan suka tarwatsa su tare da kame wasu.

Dukkanin cin zarafin da haramtacciyar kasar Isra'ila take kan al'ummar musulmin palastinu da kuma keta alfamar wurare masu tsarki da take yi a kullum rana ta Allah da ma kisan musulmi, hakan na zuwa tare da cikakken goyon bayan da take samu ne kan hakan daga manyan kasashen larabawa.

3664928


captcha