IQNA

Taro Kan Masanan Iran Da Senegal Karo Na Biyu

22:20 - November 20, 2017
Lambar Labari: 3482119
Bnagaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro karo na biyu kan masana na kasashen Iran da Senegal wato Allamah Tabataba'i da sheikh Malik Se.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labarai na hulda da jama'a a cibiyar yada al'adun uslucni ya habarta cewa, an gudanar da zaman taro karo na biyu kan masana na kasashen Iran da Senegal wato Allamah Tabataba'i da sheikh Malik Se a garin Tais na Senegal.

Bayanin ya ce wannan taro shi ne karo na biyu da ake gudanar da shi, domin kara karfafa alaka ta ilimi tsakanin masana na kasashen Iran ad Senegal.

Wannan babban malami na kasar Senegal Sheikh Malik Se yana daga cikin fitattun malaman kur'ani da suka rayu a Senegal a hekaru da suka gabata, wanda kuma ya yi rubuce-rubuce kan ilmin kur'ani, kamar yadda shi ma Allamah Tabataba'i ya kasance daga cikin manyan malaman kur'ani a Iran.

3664899



captcha