Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar kula da harkokin al'adun muslunci cewa, a jiya bayan sanar da rasuwa babban malamin addini Sheikh Mukhtar Bamba malamin darikar Muridiyya a Senegal an saka karatun kur'ani da sautin Karim Mansuri a gaban karamin ofishin jakadancin Iran a Dakar.
Sheikh bamba mutum ne da ya yi suna wajen nuna cikakken goyon bayan juyin juya halin muslucni a Iran da kuam marigayi iam Khomeni (RA).
A kwanakin baya wannan malami ya gana da shugaban cibiyar Ahlul bait (AS) Sheikh Hassan Akhtari a birnin Tuba, inda ya bayyana cewa al'ummar Senegal suna cike da kaunar juyin Islama akasar Iran da kuma marigayi Imam Khomeini (RA).
Tun bayan sanar da rasuwarsa a jiya, an sanar da jyayi a fadin kasar baki dangane da rasuwar tasa.