IQNA

Gwamnatin Sahyuniya Ta Dauki Tsauraran Matakan Tsaro

23:08 - January 12, 2018
Lambar Labari: 3482291
Bagaren kasa da kasa, jami’an tsaron haramtacciyar kasar sra’ila sun dauki kararan matakan tsaro a dukkanin yankunan Palastinawa domin hana gangami da bore.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Safa na Palastine ya habarta cewa, tun bayan furucin da Trump ya yi kan quds a cikin watan da ya gabata, al’ummar palastine ke ci gaba da nuna rashin amincewa da kudirin nasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa, kungiyoyin palastinawa ‘yan gwagwarmaya suna kiran al’ummar palastinea  kowane mako da su fito domin nuna rashin amincewarsu da wannan kudiri, musamman a ranakun Juma’a.

A yau ma kamar kowace Juma’a dakarun yahudawa sun shirya tsaf domin afkawa kan palastinawa, domin hana gudanar da gangami ko bore, inda suka kame matasa a yankuna daban-daban da suka fito kan tituna suna kabbara.

Haka nan kuma sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da bugu da kulake domin tarwatsa masu jerin gwanon, kamar yadda kuma suka yi amfani da harsasan bindiga, inda suka kashe matasa biyu daga cikin palastinawa.

3681236

 

 

captcha