IQNA

Wata Musulma Ta Fuskanci Cin Zarafi A Toronto

23:42 - January 13, 2018
Lambar Labari: 3482295
Bangaren kasa da kasa, jami'an 'yan sanda sun ce suna bincike kan wata matasiya musulma ta fuskanci cin zarafi a cikin birnin Toronto na Canada.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa, Khaula Nu'uman wata matasiya ce musulma wadda ta fuskanci cin zarafi a cikin birnin Toronto na Canada a lokacin da take a kan hanyarta ta zuwa makaranta.

Wannan matashiya 'yar shekaru 11 da haihuwa ta bayyana cewa, wani mutum ya nufi inda suke a lokacin da suke tafiya tare da dan uwanta zuwa makaranta, sun tsorata, sai suka nufi bangaren da mutane suke, daga nan kuma sai ya sake dawowa ya sanya almakashi ya yanka lullubin da ke kanta kuma ya tsere.

Ma'aikatar ilimi a cikin jahar Toronto ta bayyana hakan a matsayin wani aiki na dabbanci mai matukar muni.

Tuni jami'an 'yan sanda suka ce suns higa gudanar da bincike kan lamarin, amma har yanzu ba su kame kowa ba.

Musulmi mazauna kasar Canada sun gabatar da bukata ga gwamnatin kasar Canada kan a sanya ranar 29 ga watan Janairu a matsayin ranar adawa da kyamar musulunci, domin tunawa da kisan da aka yi wa musulmi 6  a lokacin da suke yin a irin wannan rana a shekarar da ta gabata, amma har yanzu gwamnatin Canada ba ta ce komai ba kan wannan bukata.

3681345

 

 

 

captcha