IQNA

Kur'ani Tarjamar Faransanci Ya Samu Karbuwa A Senegal

16:50 - January 15, 2018
Lambar Labari: 3482300
Bangaren kasa da kasa, tarjamar kur'ani da Abul Kasim Fakhri ya yi a cikin harshen Faransanci ya samu karbuwa a Senegal.

 

Sayyid Hassan Ismati shugaban ofishin raya al'adu na Iran a Senegal a zantawarsa da Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa Abul Kasim Fakhri  daya daga cikin malaman jami'a a Tehran da ya tarjama kur'ani a cikin harshen Faransanci, wannan kur'ani ya samu karbuwa a tsakanin al'ummar kasar Senegal.

Ya ci gaba da cewa wannan aiki yana daya daga cikin ayyuka na lfahari a kasar Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci.

Abul Kasim Fakhri ya dauki tsawon shekaru kimanin 20 yana gudanar da tarjamar kur'ani a cikin Faransanci, tare da tabbatar da cewa ya yi tarjamar tasa yadda za ta bayar da ma'anar da ake bukata.

Babbar manufarsa ta wannan aiki dai ita ce samar da hanya mafi sauki ga masu fahimtar harshen Faransanci da su fahimci abin da ke cikin kur'ani mai tsarki da kuma abin da yake koyarwa.

3682077

 

 

استقبال سنگالی‌ها از ترجمه قرآن استاد ایرانی+عکس

 

استقبال سنگالی‌ها از ترجمه قرآن استاد ایرانی+عکس

استقبال سنگالی‌ها از ترجمه قرآن استاد ایرانی+عکس

استقبال سنگالی‌ها از ترجمه قرآن استاد ایرانی+عکس

 

 

 

captcha