IQNA

Wata Cibiya Daga Kuwait Za Ta Gina Masallatai 10 A Mauritaniya

16:56 - January 15, 2018
Lambar Labari: 3482302
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Murshid shugaban cibiyar ayyukan alhairi ta kasar Kuwait ya bayyana cewa za su gina masallatai 10 a Mauritania.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin zahraa.mr cewa, Ahmad Murshid shugaban cibiyar ayyukan alhairi ta kasar Kuwait ya bayyana cewa za su gina masallatai 10 a Mauritania a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Cibiyar gudanar da ayyukan alhairi ta kasar Kuwait tan adaga cikin kungiyoyin da suke bayar da taimako ta fuskar ayyukan addini da suka shafi ginin masallatai da kuma makarantu.

Ginin masallatai 10 da wannan cibiya za ta  akasar Mauritaniya na daga cikin ayyukan baya-bayan nan da za ta yi a cikin wata kasa ta Afirka mafi girma bayan wasu da ta yi a kwanakin baya a wasu kasashen gabashin nahiyar.

Wannan aiki dai yana da babban tasiri wajen samar da yanayi na karfafa musulmi ta fuskokin zamantakewa da kuma addini.

3682104

 

 

captcha