IQNA

An Bai Wa Birnin Quds Matsayin Babban Birnin Raya Tarihi Musulunci

19:56 - March 14, 2018
Lambar Labari: 3482474
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen larabawa ta zabi birnin Quds a matsayin babban raya tarihin musulunci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Sky News ta bayar da rahoton cewa, Khalil Farajah Rufa’i babban jami’i mai kula da harkokin tarihi na birnin Quds ya sheda cewa, a zaman da wakilan kungiyar kasashen larabawa suka gudanar a jiya a babban jinin hedikwatar kungiyar da ke birnin Alkahira na Masar, sun zabi birnin Quds a matsayin babban raya tarihin musulunci na din-din-din.

Zaman taron ya samu halartar Muhammad Mkhtar Juma’a minista mai kula da harkokin addini na Masar, da kuma Badriddini Alali, mataimakin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa, gami da wakilai daga dikkanin kasashe mambobi na kungiyar larabawa, inda suka cimma matsaya tare da amincewa da wannan mataki.

Hakan na zuwa ne a matsayin martini ga matakin da shugaban Amurka ya dauka na ayyana birnin na Quds mai tsohon tarihi na musulunci, a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kasashen duniya da dama da suka hada da na musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba, sun yi tir da Allah wadai da wannan kudiri na shugaban Amurka.

3699549

 

 

 

 

 

captcha