IQNA

An Fara Shirin Gasar Kur’ani Mai Tsarki Ta Kasar Morocco

21:30 - March 16, 2018
Lambar Labari: 3482479
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da shirin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na goma sha hudu a kasar Morocco.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na aabbir.com cewa, yanzu haka an fara gudanar da shirin gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na goma sha hudu mai taken gasar sarki Muhammad na shida a kasar Morocco a bangaren karatun tarrtili da harda.

Ma’aikatar kula da harkokin adini ta kasar Morocco c eke daukar nauyin shirya wannan gasa, wadda ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya daban-daban.

Ana kasa gasar a bangarori uku na harda da karatu da uma tafsiri, kamar yadda akwai bangarorin maza da na mata, kamar yadda kuma masu gasar shekarunsu na kamawa ne daga 10 zuwa 40.

Wannan dai  shi ne karo na goma sha hudu da ake gudana da wannan gasa ta sarki Muhammadu na shida a kasar Morocco, inda daga karshe ana bayar da kyautuka ga dukkanin mahalarta gasar, da kuma kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a gasar.

3700377

 

 

 

 

 

captcha