IQNA

An Gano Wani Shirin Kai Harin Ta’addanci A Samirra Iraki

22:34 - March 20, 2018
Lambar Labari: 3482492
Bangaren kasa da kasa, an gano wani shirin kaddamar da harin ta’addanci kan hubbarori masu tsarki a garin Samirra na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalo daga shafin sadarwa na nun cewa, a jiya jami’an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin kaddamar da harin ta’addanci kan hubbarori masu tsarki a garin Samirra wanda ‘yan ta’addan wahabiyawa suka shirya.

Jami’an tsar sun gano shirin ne bayan samun wasu bayanan sirri dangane da lamarin, kuma sun kai samame a wurin da aka samu kayan da aka shirya domin kai harin, da suka hada da makamai da bama-bamai a gabshin birnin na Samirra.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake bankado irin wannan shiri na ‘yan ta’addan wahabiyawa ba da ke kokarin tarwatsa hubbaren jikan manzon Allah (SAW) Imam Al-hadi da ke birnin Samirra.

Yanzu haka dai an kame dukkanin ‘yan ta’addan da suke shirin kai harin da kuma dukkanin makaman da aka samu tare da su sanadaran hada bama-bamai da kuma wadanda suka riga suka hada.

3701526

 

 

 

 

captcha