IQNA

Saudiyya Ta Kashe Fararen Hula 17 A Hare-Haren Da Ta Kaddamar A Yemen

17:53 - March 22, 2018
Lambar Labari: 3482499
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga kasar Yemen sun tabbatar da cewa akalla fararen hula 17 ne suka rasa rayukansu da suka hada da mata da kananan yara a hare-haren da jiragen yakin masarautar saudiyya suka kaddamar a daren jiya a garin Sa'adah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, jiragen yakin gidan Sarautar Al Saud sun yi lugudan wuta a daren jiya a kan gidajen jama'a agarin Sa'ada da ke arewacin Yemen, inda suka kashe fararen hula 17 a nan take tare da jikkata wasu da dama, rahoton ya ce akasarin wadanda suka rasa rayukansu mata ne da kananan yara.

Bayan harin na sa'adah jiragen yakin gidan sarautar Saudiyya sun kai wani harin a birnin San'a fadar mulkin kasar ta Yemen a daren na jiya, inda suka kashe fararen hula, wanda hakan cika adadin fararen hula da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren na Saudiyya a Yemen zuwa 19 a cikin kasa da saoi 24 da suka gabata.

A jiya ne majalisar dattijan Amurka ta amince da ci gaba da taimaka ma Saudiyya wajen kaddamar da irin wadannan hare-hare a kan al'ummar kasar Yemen da sunan yaki da kungiyar Alhuthi.

3701688

 

 

captcha