IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Fada Da Tsatsauran Ra'ayi A Masar

17:58 - March 22, 2018
Lambar Labari: 3482500
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani taron karawa juna sani na kasa da kasa a kan fada da tsatsauran ra'ayin addini a birnin Alkahira na kasar Masar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na menafn.com ya bayar da rahoton cewa, taron ya guna ne karkashin kulawar kungiyar raya al'adu da bunkasa harkokin ilimi ta kasasashen musulmi ISESCO.

Taron ya samu halartar masana 50 da suka gabatar da kasidunsu, da suka fito daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da na musulmi da kuma wadanda ba na musulmi ba.

Babbar manufar taron dai ita fito da hakikanin koyarwar musulunci ta yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba, da kuma bayyana tsatsauran ra'ayi da ke haifar da ta'addanci kan cewa ba ya daga cikin koyarwar addinin muslunci.

3701684

 

captcha