IQNA

An Dakile Wani Shirin Kai Harin Ta'addanci

17:55 - March 23, 2018
Lambar Labari: 3482502
Bangaren kasa, Jmai'an tsaron kasar Iraki sun bankado wani shirin 'yan ta'addan takfiriyya na kai hari a yankin Anbar da ke arewacin kasar ta Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Saumaria News cewa, 'yan ta'addan wadanda suke da alaka da kungiyar 'yan ta'addan Daesh (ISIS) sun shirya kai harin ne a wani wurin tsaro da ke kan iyakar kasar Iraki da Saudiyya, wanda yake cikin lardin Anbar.

'Yan ta'addan sun shirya yin amfani da wasu motoci ne da suka shakare da bama-bamai domin kai harin kunar bakin wake, da nufin kashe jami'an tsaro da dama, amma jami'an tsaron na Iraki sun samu nasarar dakile shirin na 'yan takfiriyya.

Kungiyar Daesh tare da taimakon Amurka da wasu sarakunan kasashen larabawa, ta kaddamar da farmaki a Iraki a cikin shekarar 2014, inda ta kashe dubban fararen hula da jami'an tsaro, tare da mamaye wasu yankuna na kasar Iraki, tare da kafa abin da suke kira daular musulunci.

Dakarun Iraki tare da taimakon Iran, kungiyar Hizbullah d akuma Rasha, sun samu nasarar tsarkake dukkanin yankunan da 'yan ta'addan suka mamaye, da hakan ya hada har da bababr tungar da suka kafa a Mausul.

3701690

 

captcha