IQNA

Ana Samun Karuwar Kin Jinin Musulmi A Kasar Canada

18:00 - March 23, 2018
Lambar Labari: 3482503
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga kasar Canada na nuni karuwar kin jinin muuslmi a yankin Quebec na kasar a cikin lokutan baya-bayan nan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar CBS ta bayar da rahoton cewa, sakamakon wani jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar Canada, ya nuna cewa kin jinin musulmi yana karuwa a Quebec, inda fiye da kashi 70 cikin dari na mutanen yankin suna ka nuna tsananin kyamarsu ga addinin musulunci da kuma musulmi.

A ranar 29 ga watan Janairun 2017 ce wani dan ta'adda mai tsanain kiyayya da musulmi ya kai farmaki kan muuslmi a lokacin da suke yin salla a cikin masallaci a garin na Quebec, inda ya kashe masallata shida tare da jikkata wasu.

A cikin 'yan watannin da suka gabata ne musulmin kasar Canada suka bukaci a sanya ranar 29 ga watan janairu ta zama ranar fada kin jinin musulmi a kasar, amma mahukuntan kasar ta Canada sun ki amincewa da hakan, bisa hujjar cewa mutanen Quebec ba su amince da hakan ba.

3701749

 

captcha