Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin majami’oin mabiya addinin kirista a kasar Ghana ta bukaci a mika sha’anin tafiya da makarantun kiristoci ga majami’u a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan majami’a ta yi iamnin cewa, tafiyar da makarantun kiristoci a karakashin majami’io yana da babban tasiri, domin kuwa za a tafiyar da komai bisa koyarwar addinin kirista.
Haka nan bayanin ya kara da cewa, bisa la’akari da cewa addinin kirista bai amince da ayyukan sabo kamar shan giya da zinace-zinace ba, da kuma saka sutura maras mutunci ba, to ta haka majami’oin zasu tamaka matuka wajen rage barna a cikin jama’a.
Majami’ar ta Methodist wadda aka kafa a tu 1938, tana da mabiya a kasar Ghana wadanda suke yin riko da koyarwar abin da suka yi imani da shi.