Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin tashar alalam ya bayar da rahoton cewa, kotun kasar Bahrain ta tabbatar da cewa zargin da ake yi wa Sheikh Ali Salman da Hasan Sultan Ali Aswad kan yi wa Qatar liken asiri bah aka lamarin yake ba.
Kotun ta tababtar da hakan ne bayan kasa tabbatar da wasu dalilai kan hakan, kamar yadda kuma binciken da ta gudanar ya nuna sabanin haka.
Baya gahaka kuma a cikin makon nan kimanin kungiyar kare hakkin bil adama na duniya talatin da biyar ne daga kasashe ashirin da biyar suka bukaci masarautar Bahrain da ta gagaguta sakin Sheikh Ali Salman ba tare da wani sharadi ba.
Yanzu haka dai sheikh Ali Salman yana cikin shekara ta hudu a tsare a gidan kaso masarautar kama karya ta Bahrain.