IQNA

Majalisar Dokokin Ia’ila Ta Amince Da Dokar Hana Yada Ayyukan isan Falastinawa

23:56 - June 21, 2018
Lambar Labari: 3482776
Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da doka haramta yada duk wani aikin kisa ko cin zarafin Falastinawa da jami’an tsaron Isra’ila ke yi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a  zaman da majalisar Knesset ta haramtacciyar kasar Israila ta gudanar a jiya, an kada kuri’a kan daftarin dokar haramta yada duk wani kisa ko cin zarafi na jami’an tsaron Isra’ila  akan Falatinawa.

Mambobi 45 daga cikin mamobin majalisar sun amince da daftarin kudirin, yayin mambobi 42 suka ki amincewa da shi.

Dokar dai ta kunshi cewa, idan aka kama wani yana yada hotuna ko kuma hotunan bidiyo na wani aikin cin zarafi da jami’an tsarin Isra’ila suke yi kan Falastinawa, to za a daure shi daga shekaru 5 zuwa 10 a gidan kaso.

Yusuf Jabbarin daya ne daga cikin ‘yan majalisar Knesset ta Isra’ila daga cikin wakilan larabawa, wanda ya bayyana hakan da cewa yunkuri ne na boye muggan laifukan da sra’ila take akatawa kan al’ummar Palastine, kuma ba za su taba amincewa da hakan ba.

3724345

 

 

 

captcha