IQNA

An Samar Da Cibiyar Horar Da Yara Hardar Kur'ani A Lardin Sinai Na Masar

22:31 - September 14, 2018
Lambar Labari: 3482983
Bangaren kasa da kasa, an samar da wata cibiyar horar da kanana yara hardar kur'ani mai tsarki a cikin lardin Sinai na kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa shafin yada labarai Alsharq ya habarta cewa, bangaren yada addinin muslucni na ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ya kafa wata cibiyar horar da kanana yara hardar kur'ani mai tsarki a cikin lardin Sinai.

Bayanin ya ci gaba da cewa, an fara gudanar da ayyukan wannan cibiyar ne a kauyen Kharba da ke cikin gundumar ta Sinai, kafin daga bisania  fada ayyukanta zuwa sauran yankuna.

Abdulbaki Jauda kakakin cibiyar ya bayyana cewa, babbar manufar samar da cibiyar dai ita ce kwadaitar da yara zuwa ga hardar kur'ani mai tsarki.

3746653

 

captcha