Kamfanin dillancin lbaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, an raba kwafin kur'anai da kuma littafan addini a kasar Uganda a lokacin gudanar da tarukan Maulidin manzon Allah.
Tarukan dai ana gudanar da su ne a birane daban-daban da musulmi suke musamman ma a birnin kapala fadar mulkin kasar, inda musulmi da dama suke rayuwa a cikinsa.
Baya ga kwafin ur'anai akwai littafai na addini da suka shafi na tarihin muslunci da kuma na sanin hukunce-hukunce da sauransu, domin raba wag a makarantun addini.
Kasar Uganda na daga cikin kasashen gabashin Afrika da suke da kyakkyaawar alaka da kasar Iran.