IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ba Ta Amince da Komawar 'Yan Rohingya Ba

22:49 - November 14, 2018
Lambar Labari: 3483126
Hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci ganin kasar Bangaladesh ta dakatar da kokarin mayar da al'ummar Rohinga zuwa kasar Mayanmar da karfi

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugabar hukumar kare hakkin bil'adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta fada a jiya Talata cewa; Idan 'Yan Rohinga su ka koma gida a yanzu, to rayuwarsu za ta fuskanci hatsari.

Bachelet ta ci gaba da cewa; A kodayaushe hukumar kare hakkin bil'adaman ta Majalisar Dinkin Duniya tana samun rahotanni akan yadda ake ci gaba da cutar da azabtar da kuma sace 'yan Rohinga a can kasar Myanmar.

A shekarar da ta gabata hukumar kare hakkin bil'adaman ta Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojojin kasar Myanmar da hannu a yi wa al'ummar musulmin kasar kisan kiyashi, sannan ta bukaci da a hukunta janar-janar guda biyu na kasar.

Fiye da musulmin Rohinga dubu shida ne masu tsauran ra'ayin addinin Bhuddah suka kashe a kasar ta Mayanmar tare da tilasta wa wasu da adadinsu ya kai miliyan guda yin hijira.

3763930

 

 

captcha