IQNA

Tattaunawar Bin Salman Da Pomeo Ta Wayar Tarho

23:12 - March 20, 2019
Lambar Labari: 3483477
Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya tuntubi sakataren harkokin wajen Amurka ta wayar tarho.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a jiya yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya zanta da sakataren harkokin wajen Amurka mike Pompeo ta wayar taroho, inda suka tattauna kan lamurra da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, da ma wasu batutuwa na kasa da kasa.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka tattauna kamar kowane kowane lokaci batun kasar Iran shi ne na farko, da kuma sanin hanyoyin da za su bi wajen karya ta, da kuma haifar mata da matsaloli ta kowace fuska.

A halin yanzu dai gwamnatin ta Saudiyya ita ce kasa ta farko a duniya wadda ta fi kowace kasa sayen makamai, sakamakon yadda Amurka da Isra'ila suke tsorata ta da Iran, inda a cikin shekarar da ta gabata ta kulla cinikin makamai na dubban daruruwan biliyoyin daloli, wanda kuma hakan duk yana da cikin shirin Bin Salman.

3799177

 

 

 

captcha