IQNA

Jagora: Shekarar 98 Ta Nasara Ce A Kan Yakin Tattalin Arziki

23:31 - March 22, 2019
Lambar Labari: 3483480
Jagoran juyin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar makiyan Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kaddamar da yaki ne na tattalin arziki a kanta, sai dai cikin yardar Allah za ta yi nasara a kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a yammacin jiya Alhamis a gaban dubun dubatan al'ummar Iran a haramin Imam Ridha (a.s), Limamin Shi'a na takwas da ke birnin Mashad don tunawa a ranar farko na sabuwar shekara ta 1398 hijira shamsiyya, inda ya ce: Makiya sun kaddamar da yaki na tattalin arziki ne a kanmu. Da yardar Allah za mu yi nasara a kansu, to sai dai akwai bukatar mu ma mu yunkura.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi watsi da wasu farfaganda da ake yadawa ne na kaddamar da yaki na soji a kan Iran din a cikin wannan sabuwar shekara inda ya ce: Makiyan al'ummar Iran, baya ga abubuwan da suke yi a fili, har ila yau kuma sun kaddamar da yaki na kwakwalwa don nufin razanar da al'umma da kashe musu gwiwa. Don haka bai kamata a damu da wadannan farfagandar ba.

Yayin da ya koma kan batun yarjejeniyar nukiliya da Iran ta cimma da wasu kasashen Turai kuwa, Ayatullah Khamenei yayi kakkausar suka ga irin rikon sakainar kashi da rashin cika alkawarin da kasashen Turai suke yi, yana mai kiran jami'an kasar Iran da kada su damfara dukkanin fatansu da Turawan don kuwa su abin dogaro ba ne.

Har ila yau Jagoran yayi kakkausar suka ga matsayar da kasashen Yammaci da kafafen watsa labaransu kan kisan gillan ta'addancin da aka yi a musulmin kasar New Zealand a wasu masallatai biyu na kasar inda yake abin kunya ne irin yadda suka gagara kiran wannan danyen aiki a matsayin aikin ta'addanci.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya soki siyasar kasashen Yammaci dangane da irin goyon bayan da suke ba wa kasar Saudiyya cikin danyen aiki da kisan gillan da take aikatawa a kasar Yemen. Kamar yadda kuma yayi kakkausar suka ga kokarin da kasashen Yammacin suke yi na gina wa Saudiyyan cibiyoyin nukiliya da kuma na kera makamai masu linzami duk kuwa da danyen aikin da take aikatawa, sai dai ya ce hakan ba wai yana bakanta masa rai ba ne, don kuwa ya san cikin yardar Allah nan ba da jimawa ba dukkanin wadannan makaman za su koma hannun musulmi mujahidai masu jihadi a tafarkin Allah ne.

 

3799337

 

 

captcha