Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Qods Al-arabi cewa, jami’an tsaron kasar Ausralia sun cafke wani matashi dan asalin kasa bayan da yay i barazanar kawa musulmi hari a cikin masallaci tare da kashe su.
Yaron wanda ya fito daga jahar Victoria ya yi wannan barazana ne a cikin shafin sadarwa na yanar gizo, inda ya bayyana kin jinin muslunci da muuslmi.
Jami’an ‘yan sandan sun yaron bai wuce shekaru 14 da hahihuwa ba, a kan haka an sake a matsayin belin har zuwa ranar da za a kawo shi kotu.
Wannan na zuwa ne bayan mako guda da kai harin da yay i sanadiyyar yin shahadar masallata kimanin 50 a wani harin da aka kai musu a masallacia kasae New Zealand.