IQNA

An Girmama Shahidan New Zealand a Kasar Australia

23:36 - March 22, 2019
Lambar Labari: 3483482
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Australia sun girmama shahidan New Zealand ta hanyar yi musu sallar mamaci daga nesa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalyo daga kamfanin dillancin labaran Anatoli cewa, a daruruwan masallatai musulmin kasar Australia sun girmama shahidan New Zealand ta hanyar yi musu sallar mamaci daga nesa tare da yi musu addu’oi.

Talha Buzukurat daya daga cikin musulmin kasar Australia ya bayyana cewa, sun gudanar da wanan salla ne domin girama wadannan bayin Allah ad suka yi shahada a lokacin da aka kashe biza zalunci suna cikin bauar Allah.

Ya ce dukkanin masallatan kasar Australia an gudanar da wannan salla, kuma wannan mako ne na nuna juyayi da taya iyalan wadanda suka yi shahada a New Zealand juyayi.

A yau Juma’a a dauki kwararan matakai a dukkanin masalatan Juma’a  a kasar ta Australia, domin kare musulmi daga duk wata barazana daga masu kyamar muslunci.

3799423

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha