Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Sky News ta bayar da rahoto cewa, a cikin wannan wata na ramadana ana shirin gudana da buda baki mafi girma a kasar Masar a yankin Ginas mai tazarar kilo mita 45 daga birnin Alkahira.
Khalen Husni ya ce wannan buda baki zai zama irinsa na farko da za a gudanar a wannan yankin, inda dubban daruruwan jama’a za su halarta kuma za su ci abincin da za a tanada.
Tun a cikin shekara ta 2015 ce daia aka ayyana wannan yankin mai tazarar kilo mita 45 daga birnin Alkahira ya zama sabon birnin kasar, a cikin yankin Sharm sheikh na shakatawa.